Daga Sadik Lamin Hassan
Majalisar Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman Ta Fitar Da Sanarwar Cewar Sarkin Katsina Zai Dawo Gida Najeriya A Ranar Lahadi Mai Zuwa 30 Ga Watan Oktoba, 2022 Daga Kasar Burtaniya Da Ya Je Domin Duba Lafiyarsa.
Bayanin Hakan Na Kunshe A Cikin Wata Takardar Mai Taken Dawowar Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman Daga Ƙasar Waje, Wadda Alhaji Sule Mamman Dee, Sarkin Tsaftar Katsina Ya Sanyawa Hannu A Madadin Majalisar.
Kamar Yadda Ta Nuna Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman Zai Dawo Najeriya A Ranar 30 Ga Watan Oktoba Daga Birnin London, Inda Zai Sauka Abuja.
Ranar Litinin Mai Martaba Sarkin Zai Sauka Filin Sauka Da Tashin Jiragen Sama Na Malam Umaru Musa Yar’adua Dake Katsina Kuma Za’a Gudanar Da Addu’oin Na Musamman Na Allah Ya Kara Wa Sarki Lafiya.