Kungiyar masu hada_hadar tura finafinan Hausa ta jihar Kano, ta koka dangane da rashin tallafawa. Yankungiyar domin inganta harkokin kasuwancinsu na Yau da kullum.
Shugaban kungiyar na jihar Kano Kwamaret Anas Tijjani Abdullahi ne,ya bayyana haka ga manema labarai dangane da halin da kungiyar ta samu kanta a ciki Wanda ya gudana a ofishinsa dake kasuwar Bata anan Kano.
Anas Tijjani Abdullahi, yace tallafawa Matasan kungiyar zai kara musu karsashi da kwarin gwiwa kamar yadda ake yiwa kungiyoyin kasuwanni,yace kungiyar masu sana,ar tura finafinai ta jihar Kano tana bin dokokin hukumomin dake da alhakin fannin hadin kan daya kamata, musamman wajen yiwa mutumin dake da sha,awar shiga wannan sana,a.
Shugaban kungiyar ya jaddada kudirin kungiyar na kawo sabbin tsare tsare da zasu taimakawa alummar dake wannan jihar da ma wadanda suke shigowa domin Neman ayyukan dogaro da kai.
Kwamaret Anas yace,kungiyar ba ta barin wani baragurbi ya shigo kungiyar, kasancewar akwai matakai da hukumar tace fanafinai ta zartar ga duk mai sha,awar shiga sana,arsu,kuma, basa amincewa wani batagari ya shigo kungiyar.
Daga karshe Shugaban kungiyar ya shawarci yankungiyar dake halin da basu kamata ba,musamman masu tura fanafinan batsa da doka ta yi hani akansu,Wanda yace, kungiyar ta tanadi hukunce hukunce ga duk Wanda ta samu da laifikan da basu dace ba,za ta yi gaggawar daukar matakin da ya kamata akansa ko kuma, cinsa Tara Dai Dai da laifinsa.
Anas Abdullahi, yace,kungiyar ta bijiro da managartan tsare tsaren da su kara taimakawa jihar Kano ta fannin harkokin bunkasar tattalin arzikin jihar Kano da ma Kasa baki daya.
/Cov/Ibrahim Sani gama./
Gaskiya ne wannan tsarin Yayi sosai