Daga Faiza Iliyas Saeed,
Ko wacce ranar 24 ga watan october ranace da Hukumar lafiya ta duniya ta ware matsayin ranar yaki da cutar shan inna watau (Polio) Wakiliyar mu Faiza Iliyas Saeed ta zagaya Cibiyoyin dake bada rigakafin cutar da wasu asibitoci dake birnin tarayuar Abuja.
A tattaunawar Faiza da Sa’adatu ta shaida mata cewa, “ta gamu da larurar tana’yar shekara bakwai da haihuwa, abin da ya sa kenan ta dage da yi wa dukkan’ya’yanta bakwai rigakafin cutar”. Matar wadda’ yar asalin jihar binuwai ce a tsakiyar najeriya, ta ce ta zabi ta yi sana’a sabanin yin bara don ta taimaka wa ‘ya’yanta su samu rayuwa mai kyau. Kadan ya rage kawar da cutar ta foliyo wadda kwayar cuta ke haifarwa daga duniya baki daya. A yanzu ta fi kamari a kasashen Pakistan da Afghanistan.