Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya, INEC ta ce tsarin a kasa a tsare, a raka ba zai yi aiki ba a zaɓen bana.
INEC ta shaida hakan ne a wata tattaunawa da BBC ta yi da jami’arta, a ci gaba da kawo muku bayanai kan muhimmanci abubuwa da ya kamata a sani ko tunatarwa kafin ranar zaɓe.
Hukumar INEC ta ce a yanzu sai dai a ce a kasa a tsare a rumfar zaɓe, saboda komai zai kasance cikin na’ura wanda za a ke aikewa kai-tsaye zuwa cibiyar tattara sakamako.
Hajiya Zainab Aminu Abubakar da ke magana da yawun hukumar ta ce ta yanar gizo za a rinƙa aike sakamakon zaɓen.
BBC ta duba abin da ake sa ran masu kaɗa kuri’a za su yi don ganin an yi zaɓe mai tsabta, cikin lumana da nasara da adalci.
Duk irin shirin da hukumar zaɓe da sauran hukumomin ƙasar suka yi don gudanar da zaɓe mai inganci, ana ganin tilas su ma masu zaɓen sai sun bayar da ta su gudunmawar ta hanyar gudanar da lamurra cikin kimtsi.
Kuma ko shakka babu, yanzu haka ‘yan Najeriya da dama suna nan cike da zummar fita su kaɗa kuri’unsu a zaɓukan da ke tafe, shi ya sa Hajiya Zainab Aminu Abubakar, ke tunasar da cewa;
“Ana bukatar duk wanda ya yi rajistar zaɓe ya nemo katin zaɓensa, ya kakkabe ya adana. Saboda a ranar zaɓe a fita, a je a kaɗa kuri’a.”
Sannan jami’ar ta ce, da zarar mutane sun kada kuri’arsu, idan sun zaɓi su koma gidajensu, sai su tafi.
Idan kuma sun zaɓi su tsaya a rumfar zaɓe, su duba yadda ake gudanar da zaɓe har a kammala, za su iya tsayawa.
Amma fa komai ta intanet za a yi “da zarar sakamakon ya hau yanar gizo, ba za a iya canza shi ba, ko a lalata shi ko kuma a kawo wani sauyi a sakamakon zaɓen ba”.