Kungiyar masu hada hadar wayoyin hannu ta jihar Kano ta Sha alwashin bijiro da managartan tsare tsare don hada kan yan kungiyar da ci gaban kasuwanci a fadin jihar Kano.
Mataimakin Shugaban kungiyar reshen kasuwar Bata Alhaji Abba Garba sufi ne ya tabbatar da hakan azantawarsa da manema labarai dangane da cikar wayar hannu shekaru Ashirin da zuwa Najeriya.
Abba sufi yace a shekaru Ashirin da aka dauka na zuwan waya kasarnan ya samar wa matasa ayyukan yi domin dogaro ga kawunansu dama tallafawa alumma da iyalansu a harkokin rayuwa na yau da kullum.
Kwamared Abba surfing yace kungiyar wayoyin hannu ta jihar Kano ta bijiro da wasan kwallon kafa domin Sada zumunta tsakanin yayanta dake kananan hukumomi 44 a jihar nan, Wanda yace kungiyar ta gayyaci shugabanni daga fannoni daban daban ciki har da gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi umar Ganguje khadimul Islam.
Ya bayyana cewar za a gudanar da wasannin ne a filin wasanni na sani Abacha dake kofar mata domin ganin an aiwatar da wasannin cikin nasara da kwanciyar hankali tare da baiwa wadanda suka samu nasara sakamako.
Ya kuma bayyana cewar yin hakan zai karawa sauran yan kungiyarsu karsashi da kwarin gwiwa da samun zaman Lafiya da juna.
Abba sufi ya kara da cewar daga cikin nasarar da hada hadar wayoyin hannu ta jihar Kano ta samu Shi ne shigowar Bankuna kasuwar ta hanyar baiwa yayanta rancen jari domin bunkasar tattalin arzikin kasuwar su.
Sai dai ya koka dangane da rashin hadin kai da goyon baya da suke samu daga wajen jamian tsaro ta fuskar tuhumar yayan kungiyar musamman wajen tantance waye mai laifi tsakanin mai saye da mai sayar da wayoyi a kasuwar .
Daga karshe ya yabawa yayan kungiyarsu bisa hadin kai da goyon baya dari bisa dari da suke baiwa kungiyar tare da yi musu fatan samun nasara gasar wasan kwallon kafa da za a fafata a jihar nan.
Masha Allah, munagodiya