1. Fada maki gaskiya da baki shawara maikyau wacce zata amfaneki duniya da lahira,
2. Galibin masu sonki da gaske basuyi maki hidin-dimu na kudi da sauran abubuwa, ina nufin bazai maki karyaba
3. Zaku iyayin fada akai-akai, amma ko kunyi fadan bazai rufe ido ya gaya maki bakaken maganganu ba ballan tana zagin iyayenki,
4. Kishi! Zai riqa kishinki bazai iya jure koda yaga kinyi wata shiga marar kyauba kin fita, balle yaganki da wasu maza marar mutunci harma abokai mata marar kamun kai,
5. Zai iya hakurin wasu abubuwa idan kimmai na rashin kyautawa, musamman idan kin nunamai kinyi kuskure kin bashi hkr, bazai jada tsauri ba kuma zai girmama iyayenki,
6. Bai kiranki wani waje danku hadu, gidan ku zai riqa zuwa kuma baijin tsoron haduwa da mahaifinki ko yayyenki,
7. Zai riqa maki maganar auren ku, kuma idan kuna magana zai riqa dauko maki magana mai amfani bata shirme ba da shiririta,
8. Idan zai yabeki zai yabi halinki da tarbiyyar gidan ku, bazai kama yabon halittar jikin ki ba idamma zaiyi sai baka rasa ba,
9. Idan kin tambayeshi me yasa yake sonki, zai fada maki tarbiyyarki da mutuncin gidan Ku da tsaftarki ko kokarin neman iliminki,
Bazai fada maki dan kyawon surar jikinki ko fuskar kiba kawai,
10. Zai kula dake sosai ta ko wace hanya, duk runtsi duk wuya zai baki kulawa, idan kinyi fushi zai baki hkr ya lallasheki, kuma komai yayi maki na kyautatawa zai manta da yayi maki, balle har yayi maki gori wataran.