Daga Jamila Sulaiman Aliyu
Jami’ar tarayya ta dutsimma (FUDMA) ta nuna gamsuwarta da tsarin da makarantar kwalejin ilmi ta Aminu Kano tayi don tunkarar fara bayar karatun digiri a kwasa kwasai goma sha daya da suka samu sahalewar su fara gudanarwa jingine ta Jami”ar.
Shugaban Jami”ar tarayyar farfesa Arma’ya’u Bichi ne ya bayyana hakan Yayin da suka kawo ziyarar gani da ido domin duba tsare tsaren makarantar ko yayi daidai da ka’i’dojin da jami’ar ta gindaya tare da nuna yabo Mai yawa da kuma chan chantar kwalejin da ta ci gaba da gudanar da harkokin karatunsu ka”in da na’in tare da yabo Mai yawa akan ragin da makarantar tayi na kaso hamsin cikin dari Wanda yace hakan zai taimakawa marasa karfi su amfana da karatun na digiri.
Farfesa Arma”ya’u ya kuma Mika rokon jami’ar ga gwamnatin Kano da ta tallafawa makarantar ta fuskar matsuguni na din din din domin gwamnatin jihar Kano tayi fice wajen tallafawa ilmi in da yace fatan gwnatin Kano zata waiwayi makarantar domin tana tallafawa yan’asalin jihar .
Farfesan ya cee fannin dalibai sun tantance sun ga komai yayi dai dai da tsarin (FUDMA).
Shima a nasa bangaren shugaban makarantar Dr Ayuba ya nuna farin cikinsa da irin yabon da kwalejin ta samu duk da suna tsaka da ayyukan Samar ofisoshi da sauran gine gine domin tafikar da harkokin koyo da koyarwa na kwalejin da sukayi hadin gwiwa da Jami”ar Tarayya ta Dutsimma dake katsina tare da yin fatan alheri ga Jami,ai da ga jami’ar tarayya ta dutsimma da suka kawo ziyarar gani da ido da kuma fatan nasara.