Daga Sadik Lamin Hassan
Wasu fasinjoji biyu a sun rasa rayukansu sannan anyi garkuwa da wasu mutum uku, bayan wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari kan iyakar Magamar Jibiya a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.
Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai hari a kan iyakar ranar Asabar da misalin karfe 9:15 na dare.
Ya bayyana cewa kafin jami’an ‘yan sanda da sojoji na hadin gwiwa su fatattake su, tuni ‘yan bindigar suka tare motoci biyu a kan babbar hanyar, inda suka kashe fasinjoji biyu, tare da yin garkuwa da wasu uku.
“Kafin ‘yan sanda da sojoji su fafata da su, sun tare motoci biyu, suka kashe fasinjoji biyu tare da yin garkuwa da uku. Wannan shine hoton daya daga cikin wadanda abin ya shafa,” inji majiyar.
Duk da cewa hukumar ‘yan sanda ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba, amma rahotanni daga yankin na cewa duk da raguwar ayyukan ‘yan fashi da makami a jihar, har yanzu bangaren Jibia na cikin kakanikayi a daidai lokacin da wasu shingayen binciken jami’an tsaro da aka girke a kan titin domin duba duk wani motsin mutane, musamman kayan da aka yi fasakwaurinsu, sukayi batan dawo.
A makon da ya gabata ne dai rahotanni ke bayyana cewa shugabannin ‘yan bindiga da dama sun ajiye makamansu, inda suka mikawa gwamnatin jihar Katsina, inda suka nemi a kulla yar jejeniyar zaman lafiya da suka kulla da bangarorin biyu.
Mai baiwa gwamnan jihar shawara na musamman kan harkokin tsaro, Ibrahim Katsina ya bayyana hakan a wata hira ta musamman.
Ya ce shugabannin ‘yan bindigar sun fahimci abin da ke gabansu a nan gaba dangane da tsarin gwamnatin jihar na tabbatar da makoma mai inganci da tsarin ci gaba.