Albishirinku Maabuta bibiyar shafinmu na Aksam Media concept.
A cigaba da kawo muku labarai da Rahotanni managata masu ilmantarwa, fadakarwa da nishadantarwa, a yanzu Aksam Media zata fara kawo muku shiri na musamman mai suna “MU KOMA Gona” inda zamu dinga baku labaran Noma da kiwo tare da tattaunawa da manoma da makiyaya dan jin irin abubuwan dake wakana a fagen Noma da kiwon.
Duka dai dan farfado da sha’anin Noma da kiwo a da tabbatar dashi a matsayin sana’a.
Shirin da zai dinga zuwa muku duk yammacin ranakun Litinin A shafinmu na Aksam Media kadai zasu iya saurara.
Noma na duke tsohon ciniki kowa yazo duniya kai ya tarar.