An Binne Gawar Sarauniya Elizabeth II
Daga Walid Hari
An binne gawar Sarauniyar Ingila, Elizabeth II a Windsor Castle, kwanaki 11 bayan mutuwar ta.
A Yammacin Litinin ne dai aka gudanar da jana’izar kasar ga Sarauniyar, wadda shugabannin kasashen duniya daban-daban suka halarta.
Iyalan gidan sarautar da dama ne suka shiga tattakin raka akwatin gawar zuwa cocin St George, gabanin yi mata jana’izar karshe da iyalan gidanta suka yi mata. Sarki Edward IV ne aka fara binnewa a cocin na Fadar Windsor, wanda ya kasance a karkashin ikon gidan Sarautar na kusan shekara 1,000.
Tsoffin Sarakuna da yawa aka binne a cocin, wadanda suka hada da Sarki George IV da George III, wanda a zamanin mulkinsa ne Amurka ta samu ’yancin kai daga daular Birtaniya.
An binne Sarauniyar a kusa da kabarin mijinta Duke na Edinburg, Yarima Philip, a cocin.
Fiye da manyan baki 2000 ne suka halarci janazar Sarauniyar wadda ta riga mu gidan gaskiya a ranar Alhamis, 8 ga watan Satumba bayan shafe shekaru 96 a ban kasa.