KOSAI NA KIFI
KAYAN HADI*
Kwai
Kifi
Albasa
Attarugu
Fulawa
Maggi
Gishiri
Man gyada
*YADDA ZA KIYI*
Da farko ki samu kifi (ice fish) ki wanke sai ki zuba a tukunya ki sa maggi da gishiri da albasa ki ďora akan wuta,idan ya dahu sai ki sauke ki cicire ‘kayar shi sai ki zuba kifin da attaruhu da kuma albasa a turmi ki daka su, ki fasa ‘kwai kaďan ki zuba a ciki, ki ďauko fulawa ki zuba(hikimar sa fulawa dan ya haďe jiki ne) sai ki zuba gishiri da maggi ki juya, sannan ki dinga mulmulawa kina sakawa a cikin man gyada mai zafi kina soyawa idan yayi brown sai ki kwashe