Shugabancin kungiyar matuka motocin haya na kasa reshen Tashar malam kato,(Bus 9) ya jaddada goyan bayansa gayan bayansa ga Gwamnan jihar kano, Abba Kabir Yusuf wajen ganin an ciyar da jihar kano da Alummar ta gaba.
Ma,ajin kungiyar Alh Samaila Giredi ne ya jaddada haka a yayin da yake Zantawa da manema labarai a ofishinsa dake Tashar malam kato dake nan kano.
Yace, kungiyar ta dauki damba na ganin an ciyar da jihar kano da kuma, Alumma gaba ta hanyar tallafawa matasa da kare muradan Gwamnatin kano,musamman wajen koyawa matasa sana,ar tuki da baiwa hukumomin Gwamnati hadin kan daya dace,musamman a bangaren harkokin sufuri wajen tattarawa Gwamnati kudaden haraji yadda ya kamata.
Alh. Samaila ya nuna gamsuwar kungiyar da yadda salon Gwamnatin yake tafi musamman cikarta kwana Dari akan karagar mulki ta yadda suka kawo muhimman ci gaba da suka inganta rayuwar Alumma.
Ya kuma yi kira ga yankungiyar da su ci gaba da marawa kungiyar da Gwamnatin jihar kano baya domin samun nasarar kodirorin da aka sanya a gaba na inganta rayuwar Alumma gaba.
Ya kuma bukaci Gwamnati da ta waiwayi Tashar malam kato domin ganin an dawowa da alummar da suke cin Abinci a cikin ta ,kasancewar akwai Alumma da dama da suke gudanar da sana,oinsu a cikin Tashar wadanda kuma da nan suka dogara.
Yace, kungiyar direbobi ta malam kato ta nuna mutukar farin cikinta, bisa yadda Gwamnatin kano take da aniyar inganta Tashar malam kato ta zama ta Zamani domin nuna kishin Alummar jihar kano da yin gogayya da sauran takwarorinta jihohi da suka inganta rayuwar matasa da Alummar jihar, musamman a bangaren harkokin sufuri.
Ibrahim sani gama pyramid radio