Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja, ta kammala sauraron ƙarar da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya ɗaukaka, kan hukuncin kotun ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar.
Gwamnan dai yana ƙalubalantar hukuncin watan Satumba, wanda ya ayyana ɗan takarar jam’iyyar APC Nasiru Yusuf Gawuna ne ya yi nasara, bayan kotun ta rage ƙuri’un Abba Kabir, sama da 160,000.
Bayan sauraron lauyoyin duka ɓangarorin, sai kotun ta ce ta ajiye hukunci, wanda ake sa ran za ta sanar kan wannan shari’a a ƙasa da mako biyu.
Babban lauyan gwamnan Kano, Wole Olanipekun ya roƙi kotun ta ba da damar sauraron ƙarar da suka ɗaukaka, sannan ta jingine hukuncin ƙaramar kotu gaba ɗayansa.
Ya yi iƙirarin cewa ƙaramar kotun ta ƙirƙiro wani sabon abu, wanda ya saɓa wa duk hukunce-hukuncen da kotun ɗaukaka ƙara, da Kotun Kolin ƙasar suka taɓa yankewa a baya.
Ya kuma ce hukuncin ƙaramar kotun kuskure ne, saboda wannan ne karon farko da wata jam’iyya a Najeriya, ta shigar da ƙara ba tare da ta sanya ɗan takararta a ƙorafin da ta yi ba, kuma duk da haka aka ayyana ɗan takarar a matsayin wanda ya yi nasara.
Sai dai babban lauyan jam’iyyar APC Akin Olujimi, ya ƙalubalanci matakin inda ya ce Kotunan Daukaka Kara sun yanke ƙarara cewa, rashin sa hannu a kan ƙuri’un da aka kaɗa, daidai yake da tafka maguɗin zaɓe.
Ya ce ƙa’idojin INEC sun zartar da abin da baturen zaɓe zai yi a rumfar kaɗa ƙuri’a, ciki har da tabbatar da sa hannu da kwanan wata a bayan kowacce ƙuri’a.
Ya ce a duk inda aka samu gazawar baturen zaɓe wajen yin abin da ya dace, hakan na iya zama an saɓa wa kundin dokar zaɓe.
Game da ɗan takarar APC wanda ba a sanya shi cikin ɓangarorin da ke cikin shari’ar a ƙaramar kotu ba, Mai shari’a Akin Olujimi ya ce tabbatacciyar doka ce cewa jam’iyya ake zaɓa a duk wani zaɓe da aka yi, kuma duk wani hukunci da ya shafi jam’iyyar siyasa, to ba shakka zai shafi duk ‘ya’yanta