Kungiyar yankasuwa a nan jihar kano, sun bayyana jin dadinsu bisa baiwa musubahu shadow matsayin maitaimakawa Gwamnan jihar Abba kabir Yusuf a bangaren harkokin kasuwanni.
Alh ma,azu Dangishiri Wanda shugaban gamayyar kungiyoyin yankasuwa ne ya tabbatar da haka a wata zantawa da manema labarai a ofishinsa dake kasuwar singa anan kano.
Dangi shiri, yace, ko mutum baya son Gwamnan jihar kano, Abba Kabir Yusuf, yana da wasu abubuwa guda biyu, inda yace, Abba yana da biyayya da kuma, bibiya ga wadanda aka zalunta.
Yace, Gwamnan jihar kano Abba, yayi mutukar hangen nesa da ya dauko Alh Musubahu Shadow ya bashi matsayin mai bashi shawara akan harkokin kasuwannin jihar kano, Wanda ya San zai taka rawar gani wajen bunkasar ci gaban kasuwanci a fadin jihar kano.
Dangishiri yace, lokaci yayi da kasuwanci zai samu tagomashi na musamman domin Musubahu Shadow, mutum ne da yake da nagarta da sadaukar da kai wajen taimakawa Alumma, inda yace,yin hakan zai taimaka gaya wajen sauke nauyin da Gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya Dora masa na kulawa da harkokin kasuwanci a fadin jihar kano.
A jawabinsa daya daga cikin Dattawan shugabannin dake kula da al’amuran gamayyar kungiyoyin yankasuwa a fadin jihar kano, Alh. Bukar iliyasu Danmarafan Danmajin kano,ya bukaci kungiyoyin yankasuwa a jihar kano, da su baiwa tsarin da Gwamnati ta bijiro da shi,Na yin rijista da ma’aikatar harkokin kasuwanci, Wanda yace, yin haka zai taimakawa yankasuwa wajen ci gaban kasuwancinsu da kuma, bunkasa tattalin arzikin kasuwanci a jihar kano.
Marafan Danmajen kano,ya bayyana gamsuwarsa bisa wannan tsari Wanda yace, wannan abune da zai haifar da ‘Da’ mai ido a fannin harkokin kasuwanci.
Alh. Bukar iliyasu,yace,yankasuwar singa a shirye suke wajen ci gaba da baiwa Gwamnatin jihar kano goyan bayan da suka kamata wajen ganin an ciyar da kudirin Gwamnatin jihar kano, musamman a bangaren harkokin kasuwanci.
Ibrahim sani gama pyramid radio.