1- Ana dafa ganyen zogale da zuma a sha kamar shayi domin maganin olsa (ulcer).
2- Ana shafa danyen ganyen zogale akan goshi domin maganin ciwon kai.
3- Ga wanda ya yanke ko ya sare ko wani karfe ya ji masa ciwo, zai shafa danyen ganyen zogale inshaAllah jinin zai tsaya.
4- Ga mai fama da kuraje a jiki, ya hada garin zogale da man zaitun ya shafa.
5- Ana sanya garin zogale akan wani rauni ko gembo domin saurin warkewa.
6- Sanya garin zogale a cikin abinci yana maganin hawan-jini da kuma karama mutum kuzari.
7- Ana dafa ganyen zogale tare da sa kanwa ‘yar kadan domin maganin ciwon shawara.
8- Ga mai fama da ciwon ido zai diga ruwan danyen zogale, haka ma mai fama da ciwon kunne.
9- Macen da ke shayarwa ta dafa furen zogale da zuma dan karin nono.
10- Wanda ke fama da yawan fitsari wato cutar Diyabetis ya rinka shan furen zogale da citta kamar shayi.