Babu wata mace da ba ta so a ce fatarta tana sheki da yalki; kazalika babu wata macen da take so a ce fatarta ba ta da kyau ko daukar hankalin maza. Hakan ya sanya mata da yawa ke kashe makudan kudade wajen lura da fatar jikinsu musamman fuskar su.
Da yawa daga cikin mata kuma suna fadawa tasku sakamakon amfanin da mayukan da suke da sinadarai, wanda a maimakon kwalliya ta biya kudin sabulu sai su buge da dana-sani.
Akan hakan shirin namu na yau zai maida hankali wajan ganin ya kawowa mata hanyar da zasu gyara fatar jikin su batare da sun yi amfani da Abubuwan dake illata fata ba.
Ku kasance tare da ni Hasana B Sanusi ta cikin shirye-shiryen Aksammedia a koda yaushe dan karuwa da ireiren wadannan Abubuwan.
Hanya ta farko da zaki bi dan gyara fatar ki shine kamar haka :
1. Ki samu kukumba sai ki yayyanka ta, daga nan sai ki nika ta, sannan ki ajiye ta gefe guda. Hada ruwan Rose Water da ruwan lemon tsami ko jus din lemon tsami. Bayan nan sai ki hada su waje guda da kukumbar, sai gauraya sosai. Bayan kin yi haka sai ki shafa a fuskarki ko sauran fatar jikinki, sannan ki kwanta har zuwa wayewar gari. A lokacin da kika zo wankewa, sai ki samu ruwa mai dumi. Hakan zai kara wa fatarki lafiya da kuma sheki.
2. Hanya ta biyu ita ce, ki samu madarar shanu wacce ba a dafa ba, sai ki samu gishiri da kuma cokali biyu na ruwan lemon tsami ko ruwan jus din lemon tsami, sannan ki gauraya sosai. Bayan nan sai ki samu auduga ko tsumma mai tsabta sannan ki rika dongala kina gogawa a jikinki ko a fuskarki. Bayan nan, sai ki wanke jikinki ko fuskarki da ruwa mai dumi. Hakan zai cire miki dukkan dattin da ke makale a kofofin fatarki.
Anan zamu Dakata a wannan Rana Sai ku kasance da ni a gobe da yardar Allah dan jin cigaban shirin, da haka nake cewa kuasance da shirye-shiryen aksammedia.