A ƙoƙarinta na tabbatar da tsaro a jihar Kano, Hukumar kula da Zirga-zirga Ababen Hawa ta jiha KAROTA ta cafke wasu matasa waɗanda ake zargin ɓata-gari ne.
Jami’an sintiri na Hukumar ta KAROTA ne suka sami nasarar cafke matasan da daddare a ƙarƙashin shatale-talen Gadar Dangi da ke cikin birnin Kano.
Ɗaya daga cikin jami’an mai suna Mas’ud Ya’u Yusuf ya bayyana wa hukumar ta KAROTA yadda suka sami nasarar cafke ɓata-garin a lokacin da suka iske su suna kwance a ƙarƙashin gadar. A inda suka same su da nau’ikan kayan shaye-shaye da makamai a tare da su. Sun bayyana musu cewa yau kwanansu huɗu da shigowa garin Kano.
A binciken da Hukumar ta gudanar ta gano matasan sun shigo jihar Kano ne daga jihohin Katsina da Zamfara.
Mas’ud Ya’u ya ƙara da cewa lokacin da suke tsaka da binciken matasan sai wasu ‘yan ƙungiyar Yansintire ta wannan unguwa suka buƙaci a danƙa musu waɗannan ɓata-gari domin ƙara fadada bincike saboda sun shaidawa jami’an na KAROTA cewa ana yi musu ɗauke-ɗauke a cikin unguwar.
Yan sintirin sun bayyana cewa kwanakin baya sun sami nasarar cafke wasu ɓata-garin waɗanda suke satar kayan Gwamnati da kuma shiga gidajen al’umma domin yi musu sata.
Bayan kammala binke Hukumar ta KAROTA ta miƙa su a hannun jami’an Yansanda na ‘Yar Akwa domin faɗaɗa bincike tare da ɗaukar mataki na gaba.
Shugaban Hukumar KAROTA Hon. Baffa Babba Ɗan’agundi ya yaba wa ƙoƙarin jami’an, sannan ya yi kira ga ɗaukacin al’umma da su cigaba da kai rahoton duk wani motsi na waɗansu mutane waɗanda basu yarda da su ba domin tabbatar da tsaron unguwanni da ma jiha baki ɗaya.