Dan wasan gaba na Manchester United, kuma dan kasar Portugal Cristiano Ronalso mai shekara 37 ya sami tayin euro miliyan 300 daga wata kungiyar kwallon kafa ta Saudiyya domin ya buga ma ta wasanni na kaka biyu. (TVI and CNN Portuguesa, via AS – in Spanish)
United kuwa na tattauna ta karshe kan daukan Lisandro Martinez daga Ajax bayan da suka amince da dan wasan danda kasar Argentina mai shekara 24. (Fabrizio Romano, Twitter)
Ajax ta yarda cewa ta sha kaye kan kokarinta na hana Martinez barin kungiyar. Sai dai kungiyar, wadda ita ce zakara tsakanin dukkan kungiyoyin kwallon kafa a Netherlands, na son a biya ta fam miliyan 64. (Times – subscription required)
A yanzu Chelsea na neman dauko Presnel Kimpembe, dan wasan baya mai shekara 26 bayan da suka amince da Napoli su yi musaya da Kalidou Koulibaly, dan wasan bayansu mai shekara 31. (Guardian)
-
Chelsea ta kammala cinikin Sterling daga Man City
-
Barcelona ta amince za ta dauki Raphinha
-
Fenerbahce ta soke yarjejeniyar da ke tsakaninta da Ozil
Everton kuwa ta ce an sanar da ita kungiyar Wolverhampton Wanderers za ta amince da tayin fam miliyan 10 kan Adama Traore, dan wasan gefe mai shekara 26 da haihuwa. (Football Insider)
Kungiyar DC United ta koci Wayne Rooney sun bi sahun kungiyoyin kwallon kafa na Amurka da na Firimiyar Ingila wajen dauko Jesse Lingard mai shekara 29 bayan da ya bar Manchester United. (Marca)
Dan wasan baya na Netherlands Matthijs de Ligt mai shekara 22 ya amince a rage ma sa albashinsa domin ya iya komawa bayern Munich daga Juventus. (Bild – in German)
Barcelona ta ce ta shirya domin yin kari kan tayin da ta mika wa Bayern Munich kan dan wasanta na gaba Robert Lewandowski mai shekar 33, zuwa euro miliyan 50. (Bild – in German)