Al’ummar garin Kaduna sun gudanar da bikin sallah bana cikin kwanciyar hankali da lumana ba tare da fuskantar tashin hankali ba musamman a bangarin sha’anin tsaro.
Bayanin hakane ya zo ne a daidai lokacin da muka zanta da wasu daga cikin mazaune garin dan jin raayoyin su game da sallar ta bana.
Usman Ahmad Danmasanin Makafin Zazzau ya taba da irin kwanciyar hankali da aka samu har aka yi bikin sallah ba tare da wata barazana ba.