Sojin sama sun Kai Hari kan yan bindiga a Dazuka

Wani lugeden wutar sojin saman Najeriya suka yi a dazukan zurmi da Dan Magaji  yayi sanadiyar mutuwar  ‘yan bindiga 45 ciki har da jagoransu Dogo Rabe yayin wani sumame da dakarun suka kai maboyar ‘yan ta’addan a dazukan jihohin Zamfara da Katsina.

Yayin zantawar Abdulbaqi Aliyu da jaridar  Premium Times yace  harin sojin ya kashe ‘yan bindiga akalla 40 a yankin Birnin Magaji na jihar Zamfara.

Rundunar Sojin saman Najeriya ta ce hare-haren dakarunta a dajin sabon birnin dan Ali cikin karamar hukumar Birnin Magaji ya kashe ‘yan ta’adda 40, batagarin da wata majiya ke cewa suke aikata satar shanu a yankin.

Can a yankin Zurmi ma wani mazaunin garin Abdullahi Mamman ya ce harin Sojin ya kashe wani jagoran ‘yan bindigar Gwaska Dankarami.

A cewar Abdullahi Mamman babu tabbacin adadin ‘yan bindigar da aka kashe yayin farmakin domin kuwa adadi mai yaw ana batagarin na gudanar da wani taro ne a gidan jagoran nasu Dankarami lokacin da Sojin Najeriya suka jefa bom a cikin gidan.

Shaidar ya bayyana cewa har yanzu babu tabbacin ko jagoran na cikin wadanda aka kashe ko akasin haka.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments