Daga Walid Hari
Manchester United za ta yi amfani da wani zaɓi na watanni 12 don tsawaita kwantiragin ɗan wasan gaban Ingila Marcus Rashford, wanda zai ƙare a bazara mai zuwa idan suka kasa cimma matsaya kan sabon kwantiragi da ɗan wasan mai shekara 24 ( Daily Star on Sunday)
Har wa yau Manchester United na nazari a kan tsawaita kwantiragin golan Sifaniya David de Gea zuwa shekarar 2024. Kwantiragin ɗan wasan, mai shekara 31, zai ƙare a bazara mai zuwa ( Sunday Telegraph)
Newcastle United ta kasa ɗaukar ɗan wasan Leicester City James Maddison a bazara amma tana shirin miƙa sabon kwantiragi ga dan wasan na Ingila, mai shekara 25, a watan Janairu,m lokacin da ya rage watanni 18 a kwantiraginsa da Foxes ( Football Insider)
Tsohon kocin Tottenham da Paris St-Germain Mauricio Pochetto, yana sha’awar aiki da Aston Villa inda Steven Gerrard ke jagorantar kulob ɗin Midlands a halin yanzu ( Football Insider)