Kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, Daniel Bwala, ya nuna farin cikin sa da yadda Osinbajo da Boss Mustapha suka ce a cire daga kwamitin kamfen din APC.
Bwala, ya ce rashin goyon bayan tikitin musulmi musulmi a jam’iyyar APC ta yi ne yasa suka janye daga kwamitin yakin neman zaben
Festus Keyamo, mai magana da yawun kamfen din Tinubu/Shettima ya yi martani yana mai cewa ba a saka Osinbajo da Mustapha bane don su mayar da hankali kan aiki
Daniel Bwala, kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar ya ce ya jinjinawa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya, SGF, saboda ‘kin amincewa’ da tikitin musulmi da musulmi na jam’iyyar APC
Mun jinjinawa jarumtar Farfesa Osinbajo da Boss Mustapha saboda kin amincewa da tikitin MM ta hanyar cewa kada a saka su a kwamitin kamfen din APC. Ka da ku yarda da siyasar addini. Yan Najeriya za su raba gardama a yayin zabe.”