Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta bada sanarwar kama tsohon Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari dangane da binciken da ake yiwa Akanta Janar na kasa Ahmed Idris saboda zargin karkata kudin da ya kai naira biliyan 80.
Wani jami’in Hukumar ya tabbatarwa da manema labarai kama tsohon gwamnan tare da Anthony Yaro, shugaban wani kamfani mai zaman kan sa dangande da badakalar da ake tuhumar Idris.
Mai magana da yawun hukumar Wilson Uwajiram ya tabbatar da kama tsohon gwamnan India yace hukumar zata gudanar da bincike be visa zargin da ake wa Ahmad Idrees tsohon babban akanta na kasa.