Sharhi dangane da shigar ‘ya’yan shugabannin kasar nan siyasa

Ko da yake bawai Sabon Abu bane idan aka kwatanta da yadda shugabannin kasar nan suke gudanar da mulkin su ga Al’ummar kasar domin kuwa suna yin du mai yuwuwa ne wajan ganin sun tara wa ‘ya’yan da iyalan su abin Duniya bawai sauke nauyin da suka dauka ne a gaban su ba.

To amma Masana a harkokin siyasa sunyi duba na tsanaki akan lamarin.

Da yake a baya wasu ‘ya’yan gwamnoni da ma shahararrun ‘yan siyasa sun nuna sha’awarsu ta tsayawa takara, amma a wannan karon adadinsu ya karu, abin da masana harkokin siyasa ke kallo a matsayin yunkuri na gadar iyayensu.

Masana harkokin siyasa dai na ganin irin wannan mataki da ‘ya’ya da kuma dangin gwamnoni da manyan ‘yan siyasa suke dauka na fitowa takara a matsayin maras alfanu ga dimokuradiyya.

Sai dai akwai waɗanda suke ganin ba za a ce babu alfanu gaba ɗaya ba, musamman ganin cewa mafi yawan ƴan takarar matasa ne da ake ta fafutukar ganin suna ɗare muƙamai a madafun iko a ƙasar.

By A S Gwammaja

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments