Yan awaren kasar Kamaru basu kawo hari Najeriya ba: Rundunar Soji

 

Rundunar Sojin Najeriya tan ce babu wani hari da ‘Yan awaren da ke kokarin kafa kasar Ambazonia a Kamaru suka kai a cikin kasar kamar yadda kafofin yada labarai suka sanar.

A Wata sanarwa da kakakin rundunar sojin Birgediya Janar Onyeama Nwachukwu ya rabawa manema labarai, ta ce samun bayani dangane da harin ya sa rundunar sojin tura dakarun ta Bashu inda suka gano cewar babu gaskiya akai.

Janar Nwachukwu ya ce jama’ar yankin sun tabbatar wa dakarun cewar babu wani labari dangane da harin, sai dai wani hari da aka kai a kauyukan Obonyi 2 da Njasha wadanda ke cikin kasar Kamaru.

Sanarwar ta ce sojojin sun ceto 4 daga cikin wadanda aka kaiwa kauyukan su hari amma suka tsallake iyaka zuwa cikin Najeriya, kuma an mika su ga jami’an hukumar shige da fice

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments