Ganin babban zabe ya gabato a Najeriya,
Mai martaba Malam Muhammad Sanusi Lamido Sanusi ya yi kira ga jama’a a kan abin da ya shafi zaben 2023.
A rahoton da Daily Trust ta ruwaito tsohon Sarkin na Kano ya yi kira ga ‘Yan Najeriya da su zabi shugabanni masu nagarta da hangen nesa.
Muhammad Sanusi II ya yi jawabi a kan shugabanci a wajen wani taron maulidin Annabi Muhammad SAW a Abuja
Ustaz Muhammad Awwal Olohungbebe ya wakikci Khalifa Muhammad Sanusi, kuma ya gabatar da jawabin sa, ya yi bayani a kan shugabanci a doron Islama, yace ana bukatar wadanda za su kamanta adalci