Tottenham na ci gaba da bibiyar dan wasan Everton da Ingila Anthony Gordon, mai shekara 21, kafin watan Janairu da za a bude kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa. (Football London)
Ana sa ran tsohon dan wasan tsakiya na Ingila Alex Oxlade-Chamberlain, mai shekara 29, zai fice daga kungiyar Liverpool a kyauta a kakar wasan nan. (Fabrizio Romano)
Kungiyar ta so sayar da dan wasan tsakiyar kan farashin fam miliyan 10, a kakar wasan da ta wuce sai kuma a kai rashin sa’a ba a kammala yarjejeniya da kowacce kungiya ba. (Mirror)
Dan wasan tsakiya na Barcelona da Netherland Frenkie de Jong, mai shekara 25, ya ce kulub din La Liga ne suka kwarmatawa kafafen yada labarai bayani kan kwantiraginsa. (De Telegraaf, via Mirror)
Borussia Dortmund za ta sai da dan wasan West Ham da Leeds Raphael Guerreiro, mai shekara 28, kafin kwantiragin dan Portugal din ta kare a karshen kakar wasannin da muke ciki. (Bild – in German)
Chelsea ta damu matuka kan rashin tsayayyen lokaci ga dan wasa Romelu Lukaku a yanzu da ake gasar cin kofin duniya. Damuwar ta hada watakil darajar dan wasan mai shekara 28 ta yi kasa idan suka yi kokarin sai da shi a karshen dogon kwantiragin da yake na kyauta a Inter Milan. (Evening Standard)
Eja din dan wasan tsakiya na Dynamo Moscow Arsen Zakharyan, ya kira sha’awar da Chelsea ta nuna kan dan wasan mai shekara 19 da wasan yara. (Championat – in Russian)
AC Milan na duba yiwuwar dauko dan wasan Chelsea Hakim Ziyech, mai shekara 29, a matsayin bashi, watakil ma a kakar wasa mai zuwa za su dauko dan wasan gaba na Albania Armando Broja mai shekara 21. (Corriere Dello Sport – in Italian)
Milan ta na kuma son dauko dan wasan tsakiya na Chelsea Ruben Loftus-Cheek, mai shekara 26, bayan birgesun da ya yi a lokacin Champions League a Stamford Bridge. (Calciomercato – in Italian)