Kwararru kan harkokin tattalin arziki da masana kimiyyar halayya da zamantakewar dan adam a Najeriya da kuma talakawa sun fara mayar da martani akan alkaluman da hukumar kula da lamuran kididdiga da bincike kan sha’anin ci gaba ta kasa, wato National Bureau for Statistics NBS ta fitar a makon jiya game da matsayin talaucin da ‘yan Najeriyar ke fuskanta.
Bayanin alkaluman na kunshe ne cikin wani rahoto da hukumar ta NBS ta wallafa a ranar alhamis din da ta gabata, wadda ya nuna cewa daga cikin kiyasin yawan ‘yan Najeriya miliyan 200 da doriya, fiye da miliyan 133 na cikin kangin rayuwa saboda tsananin talauci.
Daga cikin wannan adadi in ji rahotan, mutane miliyan 86 mazauna yankin aewacin Najeriya ne.
Rahotan ya biyo bayan wani kwarya-kwaryan bincike ne na tsawon shekara guda da hukumar ta NBS ta yi a jihohi 36 da yankin Abuja bisa hadin gwiwa da wasu hukumomin ketare da suka hada da UNICEF da UNDP.
Menene raayin ku akan waccan rahoto na hukumar NBS?
Zaku iya ajiye mana raayin ku a comment da sunan ku Dan mu wallafa