An shawarci iyaye da su mayar da hankali wajen lura da al,amuran ‘ya’yansu na Yau da kullum, domin kaucewa shiga munanan ayyuka, musamman, yadda Matasa da sauran alumma suka tsinci Kansu a ciki.
Wani mai rajin ci gaban Matasa da alummar kasuwar hada_hadar wayoyin hannu dake kasuwar Bata ,Alh Hussaini Abubakar Gama ne,ya bayyana haka ga manema labarai a ofishinsa dake kasuwar.
Usaini Gama, yace,iyaye kamata ya yi su Dora’ya’yansu akan koyan sana,oi daban_daban Wanda da zarar sun kammala karatunsu na sakandire za su iya dogara da Kansu ,ya kuma,shawarci iyaye da su tashi tsaye wajen tarbiyyantar da yayansu ta yadda za su kaucewa fadawa ayyukan batagari,Wanda yanzu za ka ga Matasa suna shiga harkar save_sacen wayoyi da shan muggun kwayoyi Wanda yin hakan yanzu yana addabar alumma.
Abubakar Gama, ya kuma, ja hankalin Matasa kan su daina raina sanaoi ko Yaya suke, kasancewar duk Wanda suka gani da kudi sai da ya sha wahala sannan ya samu Allah ya sanyawa abin albarka.
Alh ussaini Gama, ya yi kira ga Gwamnati kan ta kara ribanya kokarinta wajen Samar da tallafin sanaoin dogaro da kai ga Matasa, inda yace,yin hakan zai tallafa wajen rage masu zaman kashe wando.
Ya kuma,yabawa Gwamnati bisa bijiro da tallafin da ta yi,karkashin mataimakin Gwamna Kano Dr. Nasuru Yusuf Gawuna na Matasa kimanin dubu uku.
Daga nan sai,yayi ga matasan da su tabbatar da sun mallaki katin zabe ,Wanda da shine za su sauya shugabannin na Gari a jihar da kasa baki daya.haka zalika,ya yabawa yankungiyar kasuwar wajen goyan baya da suke baiwa shugabannin kungiyar kasuwar hada hadar wayoyin hannu dake Bata.
Cov/I.S.Gama/