Shugaban gamayyar kungiyoyin kare hakkin dan adam ya bayyana cewar wannan mataki da gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin gwamna Dr.Abdullahi umar ganduje da aka dauka yayi daidai na hana yan adaidaita sahu gudanar da sufuri a fadin jihar kano daga karfe 10:00 na dare zuwa 6:00 na safe
Daga wakilin aksammedia B.imam
A karshe shugaban ya shawarci mahukunta dasu yi duba da halin lalura da zata kama bagatatan kamar kai kai mai ciki asibiti ko mara lafiya ko wani babban uziri ya kuma ja hankalin masu wannan sana’a dasu kasance masu biyayya da wannan mataki da gwamnatin ta bijiro dashi tare da shawartar mahukunta dasu duto da wani tsari da zai maye gurbin sufurin a wannan lokacip