Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa, “Shugaba Recep Tayyip Erdogan shugaba ne mai karfi kuma mai tsayin daka, yana aiki ne bisa muradun al’ummar kasarsa da tattalin arzikin Türkiye.”
Vladimir Putin ya kimanta alakar da ke tsakanin Rasha da Türkiye a taron shekara-shekara na Kungiyar Tattaunawar Valday ta Kasa da Kasa.
Da Putin ya amsa tambayar “Shekaru biyu da suka gabata ka fadi abubuwa masu kyau game da Erdogan. Shin tunaninka ya canza?”
Ya ce “Shugaba Erdogan shugaba ne mai karfin gaske kuma mai tsayin daka, yana aiki ne bisa muradun al’ummar kasarsa da tattalin arzikin Türkiye. Matsayin Erdogan kan makamashi da aikin gina bututun iskar gas na TurkStream ya tabbatar da hakan.”
Da yake nuni da cewa sun ba da shawarar kafa cibiyar rarraba iskar gas don masu amfani na Turai a Türkiye, Putin ya bayyana cewa “Türkiye ta amince da wannan tayin ne bisa nata amfanin”.
Vladimir Putin ya ce muradun Rasha da Türkiye sun kasance iri daya a fannin yawon bude ido, gine-gine da noma.
Ya kara da cewa, “A hakanan, Erdogan ba ya barin kansa ya zama nauyi ga kowa ko kuma ya yi aiki don biyan bukatun wata kasa ta uku. Yana kuma kare muradun kansa a cikin tsarin tattaunawa da mu. Türkiye da Erdogan ba kawai abokan tarayya ba ne a wannan ma’anar. Ana yanke yawancin shawarwari ne bayan dogon lokaci da tattaunawa sosai. Idan bangarorin biyu suna da sha’awar yarda, sai a cimma yarjejeniya. A wannan ma’anar, Erdogan abokin tarayya ne mai tabbas da daidaitacciyar dabi’a. Wannan shi ne daya daga cikin halayensa mafi muhimmanci.”
Putin ya ci gaba da cewa Erdogan yana kare muradun kasarsa kuma ba ya haifar da matsala ga Rasha a cikin wannan yanayi.
“Erdogan yana fafutuka ne don yanke shawarar da gwamnatinsa ta ga ya dace. Muna kuma fafutukar ganin cewa matakin da aka dauka ya dace da mu. Za mu iya samun mafita ko a cikin batutuwan da suka fi wahala kamar Siriya, tsaro, tattalin arziki, ababen more rayuwa. Mun samu damar yin hakan har zuwa yanzu.”
Idan har mun samu damar tabbatar da hakan, za mu iya tabbatar da cewa za a aiwatar da shi. Mafi mahimmancin yanayin dangantakarmu shine tabbas da daidaituwa.”