Sarkin Kano, Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero, ya nada sabbin ‘yan majalisar sa guda biyu Sarkin Bai da kuma walin Kano.
Bashir Mahe Bashir a halin yanzu shi ne Walin Kano na bakwai wanda ya gaji mahaifinsa Mahe Bashir Wali wanda yana raye amma yayi murabus daga mukaminsa saboda tsufa da rashin lafiya.
Sai kuma Mansur Mukhtar, tsohon ministan kudi kuma mataimakin shugaban Bankin Cigaban Musulunci a matsayin Sarkin Bai na tara tun bayan jihadin Usmanu Danfodio zuwa yanzu a tarihin masarautar Kano.
Mahaifinsa shi ne ‘Dan majalisar nada sarakuna da yafi dadewa a masarautar Kano tun bayan kasuwar masarautar a karni na 19.
Ya kwashe shekaru 63 a matsayin hakimi, kansila da mai nada sarakuna kafin rasuwarsa yana da shekaru 95 a duniya.