Bayan sama da shekaru 30 a hukumar NIPOST, Barista Bulus Yakubu ya zama shugaba Hukumar
NIPOST hukumar dake da hakkin sufurin kaya da lura da sakoni daga ciki da wajen Najeriya Kwanakin bayan Minista Pantami ya samar da wani sabon tsarin zamanantar da hukumar
Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya nada Barista Bulus Yakubu matsayin mukaddashi shugaban hukumar akwatin sako, ta NIPOST.
Nadin ya biyo bayan sallamar Dr. Ismail Adebayo Adewusi daga kujera sa ne.
Sanarwar na kunshe cikin jawabin da Daraktan yada labaran hukumar NIPOST, Mr Franklyn Alao ya fitar.
 Bulus ya karanci aikin Lauya a jami’ar Ahmadu Bello, daga bisani ya fara aiki a hukumar NIPOST a 1990.