Damuwa kan fifita Ukraine fiye da sauran kasashe.
Daga Walid Hari.
Wasu daga cikin shugabanin duniya sun ja hankali kan kulawa da kasashe masu fama da rikici kamar yadda manyan kasashen duniya suka damu da taimakon Ukraine.
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya na daga cikin wadanda suka ja hankali taron Majalisar Dinkin Duniya kan rigingimu masu tayar da hankali da ke gudana, inda ya bayar da misali da rikicin Isra’ila da Falasdinu da kuma halin kuncin da ‘yan kabilar Rohingya sama da miliyan daya ke ciki, Shugaba Buhari ya ce, yakin Ukraine shakka babu wani tashin hankali ne da ba a taba ganin irinsa ba tun bayan yakin duniya na biyu sai dai duk da haka kada a mance da sauran yankunan da ke fama da tashe-tashe hankula da ke bukatar taimako.
Furucin shugaban a taron majalisar na birnin New York a Amirka ya haifar da dambarwa.
Alkaluman ofishin jin kai na Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa, gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kansu sun hada sama da dala biliyan uku da rabi don taimakawa Ukraine.