Majalisun tarayya sunyi kakkausan martani ga Kungiyoyin Mata

Majalisar tarayyar Najeriya tace bukatu biyar da gamayyar kungiyoyin mata da mai dakin shugaban kasar Najeria ta jagoranta suka shigar a gaban majalisar ba zasu sami karbuwa ba a wannan karo gyaran kundin tsarin mulki da suke gudanarwa.

Mai magana da yawun majalisar wanda yake dan jam’iyar A P C ne da ya fito daga jihar Abia, Ben Kalu, shine ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja.
Duda kasancewar Aisha Buhari tana gaban kwamatin da yake aiki a kan lamarin hakan bay hana majalisar watsi da bukatar matan na Najeria ba na neman a basu kaso 20% na mukamin majalisun kasar nan da kuma kaso 35% na mukaman jam’iyun siyasar kasar nan.
Kalu ya danganta rashin samun nasarar da matan suka yi da kai kudurin nasu a takaitaccen lokaci kasancewar baije a lokacin da ya dace ba shi ya kawo rashin samun karbuwar sa a majalisun kasar.
0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments