Gwamnatin jihar jigawa tace ta kashe fiye da naira miiliyan 700 wajen gudanar da manyan ayyuka a kwalejin share fagen shiga jami’a ta jihar dake karamar hukumar Babura.
Shugaban kwalejin, Dr Hussain Shehu ya sanar da hakan ga manema labarai a Dutse.
A cewar sa, ayyukan da aka gudanar sun hadar da samarwa da kwalejin matsuguni da kewaye kwalejin da kuma gina ofishin gudanar da mulki.
Haka zalika, sauran sun hadar da gina dakin kwanan dalibai da aikin hanya mai tsawon kiloma 3 da rabi da aikin sanya ruwa harma da sanya hasken wutar lantarki.
Dr Hussain Shehu ya kara da cewar a bana ma gwamnatin jihar ta warewa kwalejin naira miliyan dari 355 a kasafin kudin wannan shekarar domin gudanar da manyan ayyuka.
Dr Hussain Shehu yayi nuni da cewar, a zancen da ake yi yanzu, hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta zamani NITDA tana gina katafariyar cibiyar fasahar sadarwa ta zamani wadda suke sa ran mayar da ita zuwa cibiyar rubuta jarabawar shiga jami’o’i da manyan makarantu ta JAMB