Kamfanonin dake buga ruwan leda da na roba a jihar Ogun sun bayyana kari a kan yadda suka saba siyar da shi a baya.
Guda daga cikin masu kamfanonin ruwan yace karin ya zamar musu dole ne kasancewar du abubuwan da suke amfani dasu wajan samar da ruwan na leda da na roba da Dollar suke siyo su.
Kazalika wani mai amfani da ruwan leda ya bayyanawa kafar yada labarai ta NAN yace ada suna siyan leda guda ta ruwan a kan kudi naira 120 zuwa 150, amma a yanzu ya koma naira 220 zuwa 250.
Ya kara da cewa yanzu haka masu siyar da ruwa dai-dai daker suke siyar da guda uku naira 50.