Kotun daukaka kara a ranar Juma’a ta amince da bukatar gwamnatin tarayya na hana aiwatar da dokar babbar kotun tarayya ta ranar 13 ga Oktoba cewa a saki Nnamdi Kanu.
Alkali Haruna Tsammani wanda ya yanke hukuncin ya bada umurnin cewa a tafi kotun koli cikin kwanaki bakwai don a yanke hukuncin karshe.
Hakan na nufin cewa za’a cigaba da rike Nnamdi Kanu a magarkamar hukumar tsaron farin kaya DSS har sai kotun kolin ta yanke hukunci.
Alkalin yayin yanke hukunci yau yace takardar da lauyoyin Kanu suka shigar don kawar da gwamnatin tarayya ba su kamshin gaskiya.