Daga Walid Hari.
Juventus na fuskantar gogayya daga Arsenal da Liverpool da Tottenham da AC Milan da kuma Barcelona a kan Marco Asensio bayan da É—an wasan na Sifaniya mai shekara 26, ya ki kara wa’adin kwantiraginsa da Real Madrid. (Calciomercato – in Italian)
Barcelona na kallon É—an wasan tsakiya na Wolves da Portugal Ruben Neves, a matsayin wanda za ta saya nan gaba domin maye gurbin Sergio Busquets, É—an Sifaniya mai shekara 34. (Sport)
Real Madrid za ta yi kokarin sayen É—an bayan Manchester City da Portugal Joao Cancelo, mai shekara 28, a bazara mai zuwa, haka kuma tana shirin zawarcin Erling Haaland a City din a 2024. (AS – in Spanish)
Har yanzu Manchester United, da Southampton da Everton na sha’awar ɗan gaban PSV Eindhoven Cody Gakpo, na Holland, kuma watakila su nemi sayensa a watan Janairu. (Football Transfers)
Liverpool na duba yuwuwar zawarcin É—an gaba na gefe Ibrahim Adel na Masar daga kungiyar Pyramids.