Kotu tayi biza ga wani matashi bisa samun sa da laifin dukkan Mahaifin Budurwar sa

DANTALA UBA NUHU KURA

Hana Saurayi Zuwa Wajen Zance Da Yin Dare Tare Da Umartarsa Ya Turo Wani Wakilinsa Dan Sanar Da Iyayen Budurwar Yayi Sanadiyar wani Matashin Saurayin Maisuna Mikaila Suleman Dake Garin Rukku a Mazabar Dan-Hassan a Karamar Hukumar Kura gurfana a gaban kotu.

Tun da fari Mahaifin Budurwar ya dawo gida da misalin karfe 11:30 na dare ya iske matashin yana tsaka da tsinkarar fure da yar tasa a lokacin ne ya tasa keyar yar tasa zuwa gida.

Bayan ya Kora yar tasa izuwa gida sai ya juya zuwa kan wannan matashi yace masa tuna nace ka turo iyayen ka kaki to ka daina zuwa gurin ta lamarin da ya fusata matashin saurayin.

Bayan ya fusata ne a take ya dare kan dokin zuciyar sa inda bayyi wata-wata ba ya dunkule hannunsa mai sanye da zoben Soyayya wani mai tsini ya naushi uban Budurwar tasa kuma ya fasa masa baya.

Fasa I hung uban Budurwar ke da wuya sai jama’a suka kai masa dauki inda again garzaya da shi wajan likita, shikuwa matashin aka Damka shi a hannun jamian tsaro.

Bayan Masoyin Maisuna Munkaila Ya Fada Ragar Jamian Yansandan Karamar Hukumar Kura Idonsa Ya Raina Fata Ya Kuma Amsa Laifinsa

Nan Take Suka Gurfanar Dashi a Gaban Kotun Shariar Musuluncin Ta Kura
Wadda  Mai-Sharia Malam Ibrahim Isa Usman yake jagoranta.

Bayaan Dan-Sanda Maigabatar Da Kara Insifecta Nasiru Dan-Sakkwato Ya Karanta Masa Takardar Tuhuma Nan Take Ya amsa laifin sa Inda Maisharia Malam Ibrahim Isa Usman
Ya Waywaya Ga Maigabatar Da Kara Insifecta Nasiru Dan-Sakkwato Cewar Ya Amsa Laifinsa
Maigabatar Da Kara Yace Mai-Shariia Munji Ya Amsa
Saidai Wanda Aka Aikatawa Laifin Iddiris Rukku Gashi a Gaban Kotun Zaiwa Kotu Karin Bayani Kan Halin Jikinsa
Kotu Ta Bashi Umarni Ya Kuma Bayyana Matsanancin Halin Da Bayan Nasa Da Kasusuwan Bayansa Ke Ciki
Na Zuwa Ganin Likita Assibitoci Daban-Daban

Yanzu Haka Dai Kotun Shariar Musuluncin Ta Kura Bisa Jagorncin Mai-Sharia Malam Ibrahim Isa Usman
Ta Daga Sahariar Zuwa Ran 17/10/2022
Dan Ganin Yadda Jikin Nasa Zai Kasance.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments