Daga Walid Hari
Majalisar wakilan Najeriya ta amince da kudirin dokar kirkiro hukuma ta musamman da ta za ta rika daukar dawaniyar hukunta masu laifukan zabe.
A wani zama da ta yi a ranar Alhamis majalisar ta karbi rahoton kwamitinta na harkokin zaɓe kan wannan kuduri.
Yanzu za a gabatar da kudirin ga majalisar dattawa kafin ya je gaban shugaban kasa domin ya zama doka.
A cewar Aishatu Dukku shugabar kwamitin kula da harkokin zabe, daftarin dokar ya nemi kafa hukuma ta musamman mai zaman-kanta da aikinta shi ne bibiyar laifukan zaɓe da sa ido domin tabbatar da cewa an yi wa kowa adalci.
Ta ce sanin kowa ne cewa galibin irin wadannan laifuka kalubale ne ga dimokuradiya.
Sannan ta ce kirkirar irin wannan hukuma ce kawai mafita, domin idan babu ita ‘yan Najeriya ba za su fahimci cewa laifi ne, mutum ya tada fitina kafin zaÉ“e ko bayan zaÉ“e ko kuma a ranakun zaÉ“e ba.
Babu kuma mamaki idan wannan hukuma ta tabbata, a ga sauye-sauye.