Rundunar yansanda ta kasa reshen jihar Kano ta Sha alwashin hada hannu da kungiyar kasuwar hada hadar wayoyin hannu ta jihar Kano domin dakile matsalar tsaro da sace sacen wayoyi da kuma kwace a jihar nan.
Kwamishinan yan sandan jihar Kano samaila Dikko ne ya tabbatar da hakan a lokacin da kungiyar hada hadar wayoyin hannu ta Kai masa ziyara da kuma bashi lambar girmamawa a ofishinsa dake nan kano.
Wakilinmu Ibrahim Sani Gama na dauke da karashen rahoton.
Kwamishinan yace yayi matukar farin ciki bisa yadda kungiyar tayi kudirin hada hannu da Rundunar domin ganin an dakile yawaitar sace sacen wayoyi musamman a wannan lokaci da alumma ta samu kanta aciki.
Samaila Dikko yace kofarsu a bude take wajen yin muamala da kungiyar duba da yawan kasuwannin siyar da wayoyi, inda yace kungiyar zata taka rawar gani wajen zakulo batagarin alumma da suke kwacen wayoyi ba gaira Ba dalili a fadin jihar Kano.
Kwamishinan ya kuma nuna farin cikinsa bisa amsa gayyatar kungiyar tun a farko domin tattaunawa da shugabanninta wajen laubo bakin zaren yawan kwacen wayoyi Wanda ya kan kai GA illata mutane.
A jawabinsa tun da farko shugaban gamayyar kungiyoyin hada hadar wayoyin hannu ta jihar Kano Alhaji Ahmad Tijjani usman yace Kwamishinan yan sandan jihar Kano ya gayyaci kungiyar da kuma tattaunawa da ita kan zargin da ake yiwa yan kasuwar Wayoyi wajen hada kai domin cefanar da wayoyin da aka sato ko kwatowa inda kuma suka fitar da rahoto na gaggawa tare da bayyana cewar Zasu bada gudunmowarsu don kawar da wannan dabia da matasa suke yi a fadin jihar nan.
Shima a jawabinsa Shugaban yace kungiyar ta Samar da cikakken kwamiti na musamman domin bibiyar masu shigowa kasuwannin wayoyin hannu domin cefanar da wayoyin da suka kwata ko suka sata daga hanun jama’a
Kazalika ya bada lambobin kiran gaggawa ga Wanda duk aka sacewa waya ko kwace masa ga kwamitin domin sanya idanu wajen gano barayin da suka sace ko kwace waya ko ina suke domin kungiyar nada rassa a kananan hukumomin jiharnan 44.
Lambobin da zaa kira sune 08065416459 ko 08039725508 ko kuma kanomofsa@gmail.com.