Gamayyar ƙungiyoyin Adaidaita Sahu na jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji. Mansur Tanimu sun kawo ziyara ofishin Shugaban Hukumar KAROTA domin nuna amincewarsu dangane da matakin da Gwamnatin jihar Kano ta ɗauka na hana Adaidaita Sahu daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.
Alhaji. Mansur Tanimu, ya bayyana cewa dalilan tsaro ne ya sa Gwamnati ta saka wannan doka saboda irin abubuwan da wasu ɓata gari daga cikin matuƙa Baburan Adaidaita Sahun suke aikatawa musamman da Daddare.
Ya ƙara da cewa su masu biyayya ne ga Gwamnati da kuma Kwamitin tsaro na jihar Kano wanda yake gudanar da aikinsa ba dare ba rana domin a tabbatar da samun zaman lafiya a jihar nan.
Ya roƙi Mambobin ƙungiyar da su zama masu bin doka da oda domin gudun faɗawa fushin hukuma