Kungiyar Gwamnonin Jam’iyar PDP ta G-5 ta kai ziyara wa Gwamnan Jihar Bauchi, Senata Bala Abdulkadir Muhammed, a matakin nemo hanyar sulhunta rikicin dake neman kawo baraka a tsakanin gwamnonin da kuma dan takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyar.
Makasudin ziyarar ta gwamnonin G-5 din shi ne neman samun damar dinke barakar da ta faru a tsakanin gwamnonin G-5 din da ‘dan takarar shugaban kasa na jam’iyar, Alhaji Atiku Abubakar, da kuma jaddada wa gwamna Bala Abdulkadir Muhammed, goyon bayansu a fafutukar da yake yi na dawowa mulki a karo na biyu.
Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike ya ce munzo ne don yin sulhu da kuma sasanta tsakaninmu,ba mu kulle kofar sulhu ba, kugiyar gwamnonin G-5 ita ce kashin bayan jam’iyyar, ba za mu rufe kofar yin sulhu ba, a shirye muke a kowani lokaci don yin sulhu.
A daya hannun, Gwamnan Jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya yi amfani da wannan ziyarar don neman gafara daga jama’a da suka nuna bacin ransu da wasu kalamai da yayi akan Fulani.
Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom
Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom
Gwamnan na Jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya ce ina so na fada cewa ba abin da nake nufi ba kenan, alokacin da aka same ni na fadi hakan, ina bada hakuri ga wanda kalamai na ya bata musu rai.
Daga bisani gwamnan Bauchi, Bala Abdulkadir Muhammed, ya yi karin haske kan ziyarar da gwamnonin G-5 din suka kawo Bauchi. Sannan wani jigo a jam’iyyar ta PDP, a Jihar Bauchi, ya jinjina wa gwamnan Bauchi, a kokarinsa na kawo sulhu tsakanin gwamnonin G-5 din da kuma Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar kujerar shugaban kasa.