A ranar 15 ga watan Disamba za a fara amfani da sabbin takardun kudin CFA a yankin Afirka Ta Tsakiya. Wannan shawarar an yanke ta ne a ranar 7 ga watan Nuwamba da muke ciki.
YAOUNDÉ, CAMEROON – Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yankin Afirka Ta Tsakiya (CEMAC) ta yanke shawarar amfani da sabbin takardun kudin CFA daga ranar 15 ga watan Disamba mai zuwa. An cimma jituwa yayin wani babban taron Kwamitin Ministocin Yankin Afirka Ta Tsakiya UMAC a ranar 7 ga watan Nuwamba.
A karshen wannan shekarar kenan za a fara amfani da sabbin takardun kudaden a kasashe shida na yankin da suka hada da Kamaru, Kwango, Chadi, Jamhuriyar Afirka ta tsakiya, Gabon da kuma Équatorial Guinea
Don haka wannan sabon fasalin kudin da aka kammala shi a shekar 2020 zai maye gurbin kudin 2002 wanda aka yi amfani da shi a cikin yankin kusan shekaru ashirin
Wani bambanci tsakanin sabbin kudaden da wadancan da za a sauya shi ne wannan karo na farko ne, inda aka bayyana duk harsunan hukuma da ke aiki a yankin CEMAC akan waɗannan sabbin rukunonin takardun kudin. Waɗannan harsunan sun haɗa da Faransanci, Ingilishi, Larabci (Chadi) da Sipaniya (Equatorial Guinea).