Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta sanar da cewa, ta baiwa jihar Anambra dake kudancin Najeriya, tallafin kayayyakin lafiya, biyo bayan mummunar ambaliyar ruwan da ta shafi mutane sama da dubu 600 a jihar a daminar bana.
Jami’in tsare-tsaren hukumar dake jihar Adamu Abdulnasir, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, hukumar tana aiki tare da jami’an lafiya a jihar, domin samar da hidimomi na lafiya da karfafa sanya ido kan cututtuka, domin tabbatar da cewa, an samar da taimakon gaggawa da zarar an gano bullar cuta.
Abdulnasir ya kuma bayyana cewa, kayayyakin tallafin da suka hada da magunguna, da na’urorin gwajin cututtuka daban-daban na gaggawa, za su tabbatar da cewa, mazauna yankunan da lamarin ya shafa, sun samu kulawar da suke bukata, domin tunkarar matsalolin gaggawa da suke fuskanta.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa, a kalla mutane 612 ne suka mutu a karshen watan Oktoba, baya ga wasu mutane miliyan 3.2 da ambaliyar ruwan ta shafa a sassan kasar, tun farkon daminar bana.