An bayyana cewa, an kasa gudanar da tattaunawar zaman lafiya da aka shirya domin dakatar da fadan da ake yi tsakanin gwamnati da ‘yan tawayen Tigray (TPLF) a arewacin kasar Habasha.
Rahotanni daga kafafen yada labaran kasar na cewa, an kasa gudanar da tattaunawar zaman lafiya da aka shirya gudanarwa a karshen mako, bayan da bangarorin suka amince da kudirin Kungiyar Tarayyar Afrika (AfB).
An bayyana cewa, ba a iya gudanar da tattaunawar ba, inda tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo da tsohon Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta za su shiga tsakani, sakamakon wasu dalilan aiki.
Kenyatta ya sanar da cewa ba zai samu damar halartar taron sulhun da aka yi niyyar gudanarwa a ranar 7 ga watan Oktoba ba saboda wasu aiyuka daban.
Ba a bayar da bayani kan lokaci ko kuma inda za a yi tattaunawar sulhun da aka soke ba.
Gwamnatin Addis Ababa da Kungiyar TPLF sun amince da shawarwarin zaman lafiya na AfB don warware rikicin da ke faruwa cikin lumana.
Tawagogin sun shirya ganawa a karon farko cikin shekaru 2 a Afrika ta Kudu a ranar 8 ga watan Oktoba.
Rikicin da ake yi tsakanin sojoji da ‘yan tawayen TPLF a kasar Habasha wanda ya fara a watan Nuwamban shekarar 2020 ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane tare da raba dubbai da gidajensu.