An kashe damisar wadda aka gano ta kashe mutane 9 a jihar Bihar ta Indiya, a wani hari.
An kai wani samame tare da ‘yan sanda 200 kan damisar da ta kashe mutane 9 a yankin Champaran na Bihar.
An kuma yi amfani da giwaye wajen aikin gano damisar. An kasahe damisar mai shekaru 3, bayan da aka gano inda take boye.
Daraktan kula da namun daji na jihar, Kumar Gupta, ya bayyana cewa an fara aikin ne saboda ana ganin damisar tana da hatsari ga rayuwar mutane.
Gupta ya ce bayan yunkurin kwantar mata da hankali, an kassara dabbar.
Indiya tana da kusan kashi 70 cikin 100 na damisa a duniya.
An bayyana cewa damisai na barin wuraren da suke zama su kai hari kan mutane yayin da yawan hare-hare a yankunan ke karuwa.
Bisa kididdigar da hukuma ta fitar, akalla mutane 40 zuwa 50 ne ke mutuwa duk shekara sakamakon harin damisa a Indiya