ISWAP sun sanar da daina karban Naira daga hanun Manoma da Masunta

Majalisar Shura ta kungiyar yan ta’addan ISWAP ta sanar da cewa ta daina karban kudin Naira daga wajen Manoma da Masuntan dake biyanta haraji saboda shirin sauya fasalin Naira da gwamnatin Najeriya tayi.

Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, ta yanke shawara sauya fasalin kudin Naira na N200, N500, N1000 kuma za’a daina amfani da tsohon takardar ranar 31 ga Junairu, 2023.

Legit ta ruwaito cewa wannan abu ya tada hankulan yan ta’addan ISWAP dake yankin Tumbus na tafkin Chadi.

Tace wata majiya mai karfi ta laburta cewa yanzu yan ta’addan kudin CFA Franc suke karba domin rage asara.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments