Daga Jamila Sulaiman Aliyu
An bayyana shiyya tarurrukan da zasu wayar da kan al’umma zai taimaka wajen samun ingantacciyar al’umma mai cike da koshin lafiya da walwala.
Shugaban kungiyar fadakarwa ta kasa reshen jihar Kano Alhaji Lawan Haruna makarfi shine ya bayyana hakan a yayin taron wayar da Kai ga ma’aikatansu wanda kungiyar yan’jaridu reshen ma,aikatar suka shirya don bawa ma,aikatansu ilmi akan abin da ya kamata suci don samun ingantacciyar lafiyar da zasu gudanar da aikinsu.
Makarfi yace hukumar fadakarwa zata dauki Shirin wayar dakai da mahimmanci dukda wa’adin aikinsa yazo karshe amma dukda hakan hukumar zata rungumi wannan tsarin.
Ya kuma ce da tun farko aka bijiro da wannan shirin wayar dakan ma,aikatan da ya jagoranci gudanar dashi duk wata don haka ya yaba da wannan namijin kokarin kungiyar yan’jaridu reshen hukumarsa.
Hajiya thuwaiba Adamu salihu ita ce shugabar kungiyar yan’jaridu reshen hukumar fadakarwa ta bayyana cewa sunga dacewar shirya wannan taronne don samarwa da ma,aikatansu hanyoyin da zasubi don su zama masu koshin lafiya tare da gayyato masana a kan ilmin kimiyyar abinci don wayar dakan ma,aikatan da sukakai shekaru talalin zuwa sama don su samu ilmin da zaisa suyi aiki cikin karsashi.
Shugaban kungiyar kwararru akan kimiyyar abinci Awwal Musa Umar yace rashin sanin ilmin abin daya kamata aci shi ke janyo yawaitar cututtuka masu yaduwaba kamar su ciwon zuciya, hawan jini, ciwon Koda, ciwon sugar, da sauransu dukkansu za,a samu raguwarsu ne ta hanyar cin abincin daya dace.
Ya kara da cewa ya kamata kowane mutum ya rika tuntubar masana a harkar kimiyyar abinci don kaucewa fada wa matsalar cututtuka ba masu yaduwa ba.wskiliyarmu Jamila sulaiman Aliyu ta labarta mana cewa taron na yini daya angudanar dashine a offishine hukumar fadakarwa Wanda kungiyar yan’jaridu reshen hukumar (NUJ) da hadin gwiwar NOA) suka shirya
Taron ya samu halattar ma,aikatan ma,aikatar dana sassan kananan hukumomi.